Almajirai Na Fuskantar Ukuba A Arewacin Najeriya

Yawaitar bara da almajirai keyi don neman abunda zasu ci da biyan bukatun yau da kullun, yasa wata kungiya mai zaman kanta ‘Gajiya Charity Foundation’ taga ya dace ta kafa Gidauniya da zata tallafa wa wadannan almajiran, da kuma fadakadda iyaye bukayar su rika sanya ‘ya’yansu a makarantun Islamiyya dake kusa dasu, maimakon kai su wasu wurare da suke fuskantar barazanar rayuwa.

An kaddamar da gidauniyar ne a fadar sarkin Keffi, a jahar Nasarawa. Shugabar gidauniyar, Hajiya Hafsat Gimba, tace sun lura cewa wasu almajiran dake bara na fadawa hannun bata gari, ana kuma amfani dasu wajen aikata miyagun ayyuka.

Shi ya sa suka ga akwai bukatar kafa wannan kungiyar don kawo karshen wannan dabi'ar da take maida al'ummah baya.

Mai martaba sarkin Keffi, Alhaji Shehu Chindo Yamusa, na uku yace su sarakuna zasu bada goyon baya wajen dakile matsalar bara da almajirai keyi.

Don karin bayani ga rahoton wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Almajirai Na Fuskantar Ukuba A Arewacin Najeriya 2'20"