AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Game Da Majalisar Dinkin Duniya
Ibrahim Garba
Ibrahim K Garba
Washington, D.C., —
Masu sauraro, assalama alaikum, da fatan an wuni lafiya. Wannan makon za a ji amsoshin wadannan tambayoyin:
A ina Majalisar Dinkin Duniya ta ke?
Mene ne dalilin saka ma ta suna Majalisar Dinkin Duniya?
Wace irin gudunmawa majalisar ke bayarwa?
Majalisar na iya magana a yi aiki da maganar?
Masu tambaya: Kawu Mairuwa Bajoga da Saleh Muhammad Isah Bajoga.
Wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Garba, ya samo amsoshin wadannan tambayoyin daga Dakta Mahadi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawan Najeriya.