Amurka Da Izra'ila Sun Yi Gwajin Makamin Kare Dangi

Hukumomin gwamnatin Amurka da ta Izra’ila, sun tabbatar da cewar gwajin makaman kare dangi da suke hadawa a jihar Alaska yayi nasara.

Firai Minitan Izra’ila Benjamin Netanyahu, ya shaida hakan a yau Lahadi, yana mai cewa makamin kare dangi na Arrow-3, zai ba kasar shi damar maida martanin ga kasar Iran ta kowane bangare.

Hukumar kere-keren makaman kare dangi ta Amurka, ta kira wannan shirin na Arrow-3 a matsayin “Cigaba mai dorewa.”

“Makamin a shirye yake, duk aka harba shi sai ya cinma buri,” a cewar Netanyahu, ya kuma kara da cewar “Duk makiyan mu su sani cewar, mun fi karfin su, zamu iya kare kanmu, kana mu iya kai musu farmaki.”

Wannan makamin na Arrow-3 da Izra’ila ta kera shine mafi karfi da zai iya wargaza duk wani hari da aka kaimata daga ko ina, wanda kamfani kera jirage sama na Amurka Boeing ya fara kerawa a shekarar 2017.