Amurka Na Neman Mafita A Diflomasiyyance Game Da Batun Iran

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce ya na kan aikin neman mafita a diflomasiyyance game da tankiyar da ake yi da Iran, wacce ake zargi da kai hari kan matatun man Saudiyya, to amma ya yi gargadin cewa muddun matakin diflomasiyya ya kasa yiwuwa, Shugaba Donald Trump "zai yanke shawarar da ta zama dole wajen cimma muradunmu."

Pompeo ya fada wa gidan talabijin na ABC News cewa yanke shawarar da gwamnatin Trump ta yi kwanan nan na tura karin sojojin Amurka da makaman yakin sama zuwa Saudiyya, zai inganta damarar sojojin ya kuma dada takura Iran.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya fada jiya Lahadi cewa kasancewar dakarun kasashen waje a yankin Tekun Pasha zai "jefa yankin cikin rashin tsaro."