Amurka Ta Girke Sojoji 2,000 A Syria

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta fada a yau Alhamis cewa kasancewar sojojin Amurka a Syria tamkar tsokanar fada da kuma keta diyaucin kasar ne

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta fada a yau Alhamis cewa kasancewar sojojin Amurka a Syria tamkar tsokanar fada da kuma keta diyaucin kasar ne.

Ma’aikatar ta yi wannan furucin ne, bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana a jawabinsa jiya Laraba cewar Amurka zata ci gaba da ayyukan da ta ke yi ta hanyar diflomasiya da soja a Syria har sai an ci nasarar yakar yan ta’adda a kasar.

Amurka na jagorar sojojin hadin gwiwa wajen kai hare hare da jiragen saman yaki a kan sansanonin ISIS a Syria da Iraq tun shekarar 2014. A watan da ya gabata ma’aikatar tsaron Amurka ta ce akwai kimamin sojojin Amurka 2,000 a Syria.