Amurka Ta Kalubalanci Sufetan 'Yan Sandan Najeriya Kan Zaben 2019

Yayin da babban zabe a Najeriya ke ci gaba da karatowa, gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa game da ayyukan Jami'an tsaron kasar a lokacin gudanar da zaben.

A wani rahoto data wallafa, Jaridar Premium Times ta ruwaito wakilin ofishin jakadancin Amurka a Najeriya Mr. David Young yana bayyana damuwa kan yadda jami'an tsaron Najeriya ke neman daukar bangare game da yadda ya dace suyi ayyukan su a lokacin zabukan dake tafe, wannan bayanin na zuwa ne a yayin wani taro da shugaban hukumar zaben Najeriya jiya Laraba,

Mr. Young yace Amurka na daukar al'amarin bada tsaro akan sha'anin zabe da muhimmanci ta yadda masu kada kuri'a zasu ziyarci cibiyoyin zabe cikin yanayin kwanciyar hankali da lumana.

Wakilin ya kuma ce akwai bukatar samar da yanayin tsaro mai kyau ga kungiyoyi da hukumomin kasa-da-kasa masu sanya ido akan yadda zaben zai wakana.

Yace tuni gwamnatin Amurka ta baiwa hukumar zaben INEC tabbacin goyon bayan da ya kamata a lokacin da jakadan na Amurka tare da jami'an diplomasiyya daga kungiyar tarayyar Turai da kasashen Jamus da Faransa suka ziyarci hukumar zaben ta Najeriya a kwanakin baya.

A don haka sai Mr. Young ya yayi fatan cewa, sabon Sufetan 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu zai bada hadin kai da goyon bayan da ya kamata domin gudanar da zaben cikin nasara.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokaci da kungiyar tabbatar da dai-daito da shugabanci na gari mai lakabin CAJA wadda ke da shalkwata a nan Kano bayyana damuwa game da yadda harkokin yakin neman zabe ke gudana a Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Kalubalanci Sufetan 'Yan Sandan Najeriya Kan Zaben 2019 - 1'24"