Hukumomin Amurka sun kama bakin haure 538 tare da tasa keyar daruruwa a dimbin samamen da suka kaddamar ‘yan kwanaki bayan kama aikin gwamnatin Shugaba Donald Trump ta 2, a cewar sakataren yada labaransa da yammacin jiya Alhamis.
Washington dc —
“Gwamnatin Trump ta kama bakin haure 538 masu aikata miyagun laifuffuka,” kamar yadda Karoline Leavitt ta bayyana a sakon da ta wallafa a shafin sada zumunta na X, inda ta kara da cewar jiragen saman soja sun tasa keyar “daruruwa.”
“Aikin tasa keyar bakin haure mafi girma a tarihi na nan tafe. An cika alkawuran da aka dauka,” a cewarta.
A sanarwar daya fitar da safiyar jiya Alhamis, Magaji Garin Newark Ras J. Baraka yace jami’an hukumomin kula da shige da fice da na yaki da fasakwabri “suka kai samame a wata cibiya dake birnin…tare da tsare mazauna yankin da basu da takardu harma da ‘yan kasa ba tare da nuna iznin kotu ba.”