Amurka Ta Lashe Kofin Duniya

APTOPIX France US Netherlands WWCup Soccer

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafar Amurka ta mata, ta lashe gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Netherland da ci 2-0 a wasan karshe da aka yi a birnin Lyon na kasar Faransa.

Wannan shi ne karo na hudu da kungiyar take lashe kofin na duniya a jeri -babu kakkautawa.

Tawagar ‘yan wasan ta lallasa takwarorinta na nahiyar turai, da suka hada da Sweden, Spain, Faransa da Ingila kafin su kai wasan karshen, suka kuma doke Netherland, wacce ita ce zakarar nahiyar.

Fitacciyar ‘yar wasan tawagar, Megan Rapinoe ce ta budewa Amurka kofar zura kwallaye bayan da ta yi nasarar buga penarti a minit na 61.

Sannan sai ‘yar wasa Rose Lavelle ta kara wata kwallo ta biyu a minti na 69, aka kuma tashi a haka.