Amurka Ta Sakawa Rasha Sabbin Takunkumi

Wata ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin (Hagu) da Shugaba Donald Trump (Dama) suka yi a watan Yunin da ya gabata a Japan

Ana sa ran takunkumin zai fara aiki kwanaki 15 bayan an sanar da majalisar dokokin kasar kan wannan mataki, wanda zai kai tsawon shekara guda.

Amurka ta kakaba wasu sabbin tukunkumi akan Rasha, saboda hannu da aka same ta da shi a sakawa wani tsohon mai leken asirin kasar da ‘yarsa guba a Birtaniya.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta nuna cewa, sabbin takunkumin, za su dakile duk wata dama da za ta ba Rasha ikon samun karin kudaden bashi ko wani taimakon daga Bankin duniya da hukumar lamuni ta duniya IMF.

Sannan za a hana duk bankunan Amurka yin huldar kudi da Rasha, baya ga wasu tsauraran matakai da Amurkan ta dauka.

Ana sa ran takunkumin zai fara aiki kwanaki 15 bayan an sanar da majalisar dokokin kasar kan wannan mataki, wanda zai kai tsawon shekara guda.

Tsohon dan leken asirin na Rasha Sergie Skripal da ‘yarsa sun sha da kyar a bara, bayan da aka saka musu guba a birnin Salisbury da ke Birtaniya.