Amurka Ta Taimakawa Kasashen G5 Sahel Da Kayan Aikin Soji

Kayan aikin soji da gwamnatin Amurka ta ba Jamhuriyar Nijar gudummuwa

Gwamnatin kasar Amurka ta tallafawa rundunar hadin guiwar kasashen G5 Sahel da wasu kayayakin ayyukan soja a ci gaba da karfafawa dakarun wannan yanki guiwa a yakin da suke kwafsawa da kungiyoyin ta’addancin iyakokin kasashen Mali Burkina da jamhuriyar Nijer.

Motoci masu silke kimanin 22 kirar MAMBA hade da land cruiser 2 na amfanin aisibitin sojoji, da wasu kayayakin gyaran motoci masu sulke ne aka hannuntawa hukumomin tsaron wannan kasa a yayin wani bukin musamman da aka gudanar a birnin yamai.

Kayan aikin soji da gwamnatin Amurka ta ba Jamhuriyar Nijar gudummuwa

Kayayyakin wadanda darajarsu ta haura miliyan 8 na dolar Amurka gudunmuwa ce daga gwamnatin Amurka domin amfanin bataliyar sojojin Nijer mai aiiki a karkashin rundunar G5 Sahel. Da yake jawabi a yayinda yake damka makulan wadanan motoci jakadan Amurka Eric P Whitaker ya bayyana burin ganin an shawo kan ayyukan ta’addanci a yankin.

Ya ce “Muna fatan kayayakin da muka bada zasu karfafawa Nijer guiwa a yukurinta na jibge kwararun askarawa masu aikin sintirin da zai karawa daukacin dakarun tsaro azamar aiki ta yadda za a tabbatar da tsaro akan iyakokin kasashen Mali Burkina Faso da Nijer.”

Da yake karbar wannan tallafi ministan tsaron kasar Nijer Pr Issouhou Katambe ya yaba da gudunmuwar da kasar Amurka ke baiwa wannan kasa da makwaftanta akai akai a fannonin da suka shafi sha’anin tsaro.

Kayan aikin soji da gwamnatin Amurka ta ba Jamhuriyar Nijar gudummuwa

A watan fabrairun 2019 kasar Amurka ta baiwa jamhuriyar Nijer motoci masu silke kimanin 60 da treloli 4 da tankoki 2 na dakon mai 2 na ruwa ba’idin wasu runhunan tamfol da naurorin kariyar sojoji da na harakokin sadarwa a fagen daga a ci gaba da karfafa matakan yaki da kungiyoyin ta’addancin yankin sahel.

Saurari cikakken rahoton da wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Taimaka Wa Jamhuriyar Nijar Da Kayan Aikin Soji-2:30"