Amurka Tana Shirin Girke Karin Garkuwar Kare Makamai Masu Linzami

Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya sanar da shirin dakile baranazar sojan da Koriya ta Arewa ke yi tare da girke karin shingayen kare kai daga makamai masu linzami.

Da yake magana jiya jumma’a a nan birnin Washington, Hagel ya bayyana cewa, shirin ya kunshi kafa wata tashar na’urar hangen makamai ta rada a Japan , ya kuma ce za a yi haka ne ganin ci gaban da Koriya ta Arewa ke samu a fasahar makaman nukiliya.

Bisa ga cewarsa, Amurka ta riga ta girke shingayen kare makamai masu linzami guda talatin a jihohin California da Alaska kuma sababbin tashoshin zasu fara aiki a shekara ta dubu biyu da goma sha bakawai.

Koriya ta arewa ta yi barazanar shiga yakin Koriyawa na biyu tare da amfani da makaman nukiliya a matsayin maida martani kan takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Pyongyang sakamakon gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da tayi a watan Disamba, da kuma gwajin makamin nukiliya karo na uku da tayi watan da ya gabata.