Amurka Za Ta Hana Shigowa Daga Brazil

Amurka za ta hana shigowa daga kasar Brazil, kwanaki biyu kafin hanin da ta sanar tun da farko ya fara aiki.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da kasar ta Brazil ta yi na sabon adadin masu mutuwa sanadiyyar coronavirus a kasar kullayaumin – wanda a yanzu ya dara na Amurka.

Jami’ai a Amurka dai ba su fadi dalilin hanzarta fara aikin dokar hana shigowa daga Brazil din ba, wadda a da sai ranar Alhamis za ta fara aiki.

Amma yanzu daga yau Talata za ta fara aiki.

A jiya Litinin ma’aikatar Lafiyar a Brazil, ta ce cutar COVID-19 ta kashe mutum 807 cikin kwana guda.

Mutane 620 ne dai ke mutuwa sanadiyyar cutar a Amurka.