Amurka Zata Tattauna da Koriya ta Arewa Idan Zata Sako Amurka Ukun da Take Tsare Dasu

Rex Tillerson Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Fadar White House tace tana iya tattaunawa da Koriya ta Arewa idan ta amince da sako Amurkawa ukun da take tsare dasu

Fadar White House ta shugaban kasar Amurka ta ce zata iya zaman tattaunawa da kasar Koriya ta Arewa ne kawai idan maganar shirin sakin Amurkawa ukun da Koriya din ke tsare da su zasu yi.

Sanarwar dai ta fito ne kwana guda bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa har yanzu Amurka na da hanyar magana da jami’an Koriya ta Arewa kai tsaye, kuma jami’an Amurka na neman a yi zaman tattaunawa.

Amma sa’o’i kadan, sai shugaban Amurka Donald Trump ya fito, yana sukar kalaman na Tillerson, yana mai cewa Tillerson yana bata lokacinsa ne kawai na yin magana da Koriya ta Arewa.

Sai dai duk da wannan furuci da Trump yayi, fadar White House ta fada jiya Litinin cewa har yanzu shugaban kasa yana da kwarin gwiwa akan Tillerson.

Da alama dai wadanan magangannu masu sabawa juna dake fitowa daga bakunan shugabannin na Amurka kan batun Koriya sun haifar da rudami a tsakanin Amurkawa.