An Bada Umurnin Bude Kasuwar Kifin Diffa

Hukumomin jamhuriyar Niger bayan wani dogon nazari sun ba magabatan jihar Diffa umurnin su bude kasuwar kifin yankin da ta yi kusan shekara hudu a rufe biyo bayan matsalar ‘yan boko haram da ta yi kamari a yankin.

A cewar Hankurau Biri Kasum, magajin garin Diffa, gwamnati ta yi zama da duk wadanda abin ya shafa, suka yi nazari akan muhimmancin kasuwar ta yin la'akari da yadda take da tasiri ga tattalin arzikin yankin ta hanyar huldar kasuwanci da kasashe makwafta irin su Najeriya, Kamaru da Chadi da suke zuwa sayen kifi, an kuma sanya jami’an ‘yan sanda da ‘yan kwastam a wajen don su lura da abinda ke faruwa.

Yanzu haka a cewar Abdulahi Roro, ya ce sauke kifin da lodin sa a kasuwar ya kankama, ana ta aikin lodin kifin zuwa wurare dabam dabam a kasar da waje, ya kuma ce ba karamin farin ciki suka yi ba ganin cewa yawancin jama’a da kasuwancin suka dogara. Ya kara da cewa an dauki kwararan matakai na tsaro da suka hada da tantance masu dako, da masu saye, da daukar kifin a mota.

Shi ma a nashi bangaren shugaban kungiyar direbobi na Diffa, Kongo Alasan ya ce suna sa ido akan duk motar da ta yi lodi tare da duba takardun ta, haka kuma ‘yan kungiyar su suni bi sau da kafa.

Ga karin bayani cikin sauti daga Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bada Umurnin Bude Kasuwar Kifin Diffa - 3'27"