An Bayyana Sabon Sarkin Gaya A Jihar Kano

  • Murtala Sanyinna

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana sabon sarkin Gaya, da zai maye gurbin marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir, wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon da ya gabata.

Biyo bayan rasuwar Sarkin Gaya a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, gwamnatin jihar ta bayyana Alhaji Aliyu Ibrahim, a matsayin sabon Sarkin Gaya.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji ne ya bayyana nadin sabon sarkin a madadin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Sabon Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim

Sanarwar nadin sabon sarkin ta ce an yi haka ne bisa karfin ikon da dokar nadin sarakuna ta shekarar 2020 da aka yi wa kwaskwarima ta baiwa gwamnan jihar.

Ta ci gaba da cewa nadin Aliyu Ibrahim ya biyo ne bayan shawarwarin da masu nadin sarki a masarautar suka gabatarwa gwamna Ganduje, shi kuma ya amince da zabin na su.

Kafin nadinsa, Aliyu Ibrahim yana rike da sarautar Ciroman Gaya, kuma da ne ga marigayi Sarkin Gaya, wanda ya rasu a ranar Laraba, 22 ga watan nan na Satumba.

Marigayi Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir

Masarautar Gaya na daya daga cikin manyan masarautu 4 da gwamna Ganduje ya kirkiro a jihar, a shekarar 2019.