An Bayyana Sunan Wanda Ya Sace Jirgin Saman Da Ya Rikito a Amurka

  • Ibrahim Garba

Gobarar jirgin da ya fadi

Hukumomi a Amurka sun bayyana wani Richard Russel dan shekaru 29 da haihuwa da cewa shi ne mutumin nan da ya yi kukan kura ya shiga gaban jirgin sama ya cilla sama, ya je ya rikito ya kashe kansa. Tuni aka fara cikakken bincike.

An bayyana mutumin nan da hukumomi su ka ce ya sace wani jirgin saman jigilar mutane a jahar Washington ranar Jumma’a da sunan Richard Russell.

Mutumin, dan shekaru 29 da haihuwa ma’aikacin kamfanin Jirgin Saman Horizon Air ne, da ke sashin kula da kayan matafiya da zakudar da jirage idan bukatar hakan ta taso. Hukumomi sun ce ya yi aiki ranar Jumma’ar, kuma ya na saye da kayan aiki, yayin da ya shiga gaban jirgin saman kamfanin Horizon Air da ke ajiye ya cilla sama.

An yi imanin cewa ya mutu bayan da ya rikito da jirgin a tsibirin Ketron, mai tazarar kilomita 48 Kudu da Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Seattle-Tacoma, al’amarin da ya haddasa wata babbar wutar daji. Hukumomi sun ce da niyya ya kashe kansa.

Jiya Asabar hukumomin bincike na tarayya su ka fara bincken yadda aka sace tare kuma da gwara jirgin da kasa da daren ranar Jumma’a daura da Seattle.