An Bude Sansanin Masu Yiwa Kasa Hidima na Yola

Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima A Yola

An sake bude sansanin horas da masu yiwa kasa hidima na Yola fadar jihar Adamawa, bayan rufe shi shekaru uku da suka gabata sakamakon rikicin Boko Haram.

Bude sansanin yazo ne biyo bayan nasarar da sojojin Najeriya ke samu a kokarin murkushe ayyukan ta’addanci.

Da yake wa Muryar Amurka bayanin matakan da suke dauka don kau da fargabar sha'anin tsaro da wasu masu yi wa kasa hidima ke da ita. Bayan da sakataren da ke horas da masu yiwa kasa hidima a jiha mallam Mohammed Abubakar ya ce hukumar zata gayyaci shugabannin kabilun sassan Najeriya don tabbatar masu da tsaron lafiyarsu.

Shugaban hukumar ya ce suna sa ran cewa masu yiwa kasa hidima dubu biyu da dari biyar zasu iso jiha domin aikin bautar kasa.

Wasu masu yiwa kasa hidima da sashin Hausa ya yi hira da su sun ce sabanin rahotanni da suke ji, sun tarar da jama'a zaune lafiya cikin kwanciyar hankali.

Domin karin bayani ga rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bude Sansanin Masu Yiwa Kasa Hidima na Yola - 2'59"