An Bukaci 'Yan Kasuwar Adamawa Su Gujewa Tashin Gobara

  • Ladan Ayawa

Gobara

An bukaci 'yan kasuwa da su rika kula da kashe hasken wutan lantarki a duk lokacin da zasu rufe shagunansu domin gujewa tashin gobara.

Wannan kiran yana zuwa ne biyo bayan karin samun tashe-tashen gobarar da ake samu a cikin kasuwanni a jihar Adamawa. Shugaban ‘yan kasuwar jihar Alhaji Mohammad Ibrahim shine yayi wannan kiran a tattaunawarsu da wakilinmu a Jihar Adamawa.

Yace gobarar baya bayan nan ce ta tashi a kasuwar Yola da kuma wani gida a Dobeli, inda aka samu asarar dukiya, yayin da wasu suka tsallake rijiya da baya, kamar yadda Malama Fatima ta shaida mana.

A jihar Adamawa kawai a 'yan watannin nan, sama da 'yan kasuwa 800 gobara ta shafa, lamarin da ya jefa wasu da dama cikin mawuyacin hali, wanda kawo yanzu babu wani tallafin da ya shigo hannunsu.

Sau tari akan danganta tashin gobarar, ga ko dai sakaci ko kuma karfin wutar lantarki. Malam Muhammad Ismail, wani Dan Jarida kuma mai sharhi da fashin baki kan al’amuran yau da kullum yace, idan aka bi ta barawo to ya kamata a bi ta mabi sawu.

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci 'Yan Kasuwar Adamawa Su Gujewa Tashin Gobara - 2’57"