An Cafke Masu Safarar Muggan Kwayoyi a Kan Iyakar Nijar

Wani jami'in tsaro

Hukumar ‘yan sandan da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta cafke wasu mutane lokacin da suke kokarin shiga kasar jamhuriyyar Niger da wasu dinbin kwayoyi.

A jamhuriyar Nijer hukumar ‘yan sandan da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi, ta cafke wasu mutane lokacin da suke kokarin shiga kasar ta kan iyakarta da jamhuriyar Benin, dauke da dinbin muggan kwayoyin wadanda suke kokarin isar da su kasar Algeria.

Mutane uku ne hukumar ‘yan sanda ta gabatar wa manema labarai, wadanda tace jami’an tsaro sun kama a tashar bincike ta garin Gaya dake kan iyakar kasashen Nijer da Benin, dauke da kwayoyi kimanin miliyan 2,900,000 wadanda suka boye a akwatunan matafiya akan hanyarsu ta zuwa kasar Aljeriya, inda su ke saran batar da su a kasuwannin wannan kasa mai makwabtaka da kasashen Mali da Libya da ke matsayin matattarar ‘yan bindiga.

Mataimakin alkali mai shigar da kara da sunan gwamnati sibstitut du procureur Garba Mahaman Kabiru ya ziyarci ofishin hukumar OCRTIS, inda aka shanya wadanan miyagun kwayoyi domin jinjina wa jami’an tsaro sakamakon wannan cafka. Ya yi kira ga gwamnatin Nijer ta dauki dukkan matakan da zasu bada damar cigaban yaki da masu sha da fataucin myagun kwayoyi, haramtacciyar sana’ar da bayanai ke nunin tana kokarin samun gindin zama a ‘yan shekarun nan a wannan kasa.

Ga wakilin Muryar Amurka a Yamai, Sule Barma, da cikakken Rohoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Cafke Wasu Mutane Dauke Da Miliyoyin Kwayoyi 2'48"