An Cimma Yarjejeniya A Taron Sulhu A Bokkos

Shugabannin al'ummomin Ron, Kulere, Mushere da Fulani sun kuma yarda cewa za a kafa kungiyar sintirin hadin guiwa na kabilun duka a Bokkos, Jihar Filato
Shugabannin al'ummomin Ron da Kulere da Mushere da kuma Fulani a yankin karamar hukumar bBokkos a Jihar Filato, sun cimma yarjejeniyar cewa zasu takaita shigar bakin da rikici ya koro daga wasu sassan kasa.

Haka kuma, sun cimma daidaiton ra'ayi a kan dakile shan miyagun kwayoyi da barasa da matasansu keyi, wadanda suka ce su na kara iza wutar fitina a yankin.

An cimma wadannan ne a wurin taron da shugabannin al'ummomin suka yi da na gwamnati da kuma jami'an tsaro kan yadda za atabbatar da zaman lafiya a Bokkos, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da fitina a Jihar Filato.

Shugabannin suka ce zasu kafa wata kungiyar sintiri ta hadin guiwa wadda zata kunshi 'yan kabilun baki dayansu, domin su rika sanya idanu kan abubuwan dake faruwa a yankin nasu.

Wakiliyarmu, Zainab Babaji, ta tattauna da shugaban karamar hukumar Bokkos, Mr. Zakka Akos, da Ardon Fulanin Bokkos, Yakubu Dabo Boro, ta kuma aiko mana da wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

An Cimma Yarjejeniya A Taron Neman Zaman Lafiya A Bokkos, Jihar Filato - 3:57