An Dakatar Da Oshiomhole Daga Shugabancin Jam'iyyar APC

Babbar kotun Najeriya dake birnin Tarayya Abuja ta bada umurnin dakatar da shugaban jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshiomhole har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar da aka shigar a kansa game da wata badakalar kudi da kuma zargin shugabancin kama karya a jam’iyyar.

Mai shari’a Danlami Senchi, ya umurci Oshiomhole ya bar ofishinsa har sai an yanke hukunci kan wannan karar.

Daya daga cikin masu shigar da kara da su ka hada da mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa maso gabashin Najeriya Komred Mustapha Salihu, ya bayyana cewa, Oshiomhole ya keta ka’idodin jam’iyya don haka bai kamata ya ci gaba da zama kan kujerar ba.

Helkwatar jam’iyyar APC a ta bakin sakataren walwalarta Ibrahim Masari, ta ce wasu da ba sa kishin jam’iyyar ne suka shigar da karar kuma Oshiomhole zai dau matakin daukaka kara.

Cikin zarge-zargen da ake yi wa Oshiomhole har da batun yadda aka kashe kudi fiye da Naira biliyan 15 a lokacin yakin neman babban zaben da aka yi a shekarar 2019.

Da ma a baya reshen jam’iyyar APC na jihar Edo ya dakatar da Oshiomhole bisa zargin raina gwamnan jihar Godwin Obaseki da kuma yunkurin nada dan amshin shatar sa ya karbi madafun ikon jihar a zaben da za a yi a bana.

A saurari cikakken rahoton a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Dakatar Da Oshiomhole Daga Shugabancin Jam'iyyar APC - 2'57"