An Dakatar Da Paul Pogba Kan Zargin Amfani Da Kayan Kara Kuzari

Paul Pogba

Za a sake wani gwajin na biyu domin tabbatar da na farko, idan kuma har aka samu Pogba da laifi, zai iya fuskantar hukuncin haramcin buga wasa na tsawon shekara hudu.

Hukumomin kwallon kafa a Italiya sun dakatar da dan wasan Juventus Paul Pogba bayan da aka zarge shi da amfani da kayan kara kuzari.

Hukumar da ke yaki da masu shan kayan kara kuzari a wasanni Nado Italia ce ta sanar da cewa gwajin da ta yi wa dan wasan ya nuna burbushin sinadarin testosterone mai kara karfin maza.

A ranar 20 ga watan Agusta aka yi wa Pogba gwajin bayan karawar da Juventus ta yi da Udinese.

Koda yake, bai buga wasan ba amma yana zaune a benci. Yanzu hukumar ta Nado Italia ta dakatar da dan wasan mai shekaru 30.

Sai dai za a sake wani gwajin na biyu domin tabbatar da gwajin farko.

Idan kuma har aka samu Pogba da laifi zai iya fuskantar hukuncin haramcin buga wasa na tsawon shekaru hudu.

Wannan dai wani karin kalubale ne ga dan wasan wanda tun bayan da ya yi kome zuwa Juventus daga Manchester United, yake ta fama da jinya.

Baya ga haka, akwai wani bincike da ‘yan sanda ke yi a Faransa kan zargin cewa wasu na kokarin su karbi kudade hannunsa.