An Dauki Matakan Tsaro A Jihar Nassarawa Bayan Asarar Rayuka

Harin da makiyaya ke kaiwa a kauyukan Taraba

Gwamnatin jihar Nasarawa tace ta dauki tsauraran matakan tsaro a yankin karamar hukumar Akwanga, bayan wani rikici da yayi sanadin rasa rayukan mutane goma sha shida a karshen makon jiya.

Lamarin ya auku ne a wani kauye mai suna Wuman, dake kusa da Andaha a karamar hukumar Akwanga, yayinda al’ummar Mada ke wani biki.

A cewar wani ganau da ya bukaci in sakaya sunansa, mutane goma sha shida ne ‘yan bindigar suka harbe har lahira.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jahar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini ya yi kira ga hukumomi su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata kisan, a kuma hukunta su.

Komishinan yada labaran jahar Nasarawa, Muhammad Jamil Zakari ya bayyana cewa, tuni gwamnati ta tura jami’an tsaro a yankin.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane 16 sun rasa rayukansu a Nassarawa-3:24"