An Fara Kidayar Kuri’u a Zaben Jihar Ekiti

Ma'aikatan zabe na shirya kayan aiki

Rahotanni daga jihar Ekiti na nuni da cewa yanzu haka an fara kidayar kuri’u na zaben gwamnan jihar da ake gudanrwa.

Jama’a sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’unsu a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a fadin jihar Ekiti.

An dauki matakan tsaro don tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba a zaben, amma duk da haka wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun yi yunkurin tayar da fituna, inda har suka fasa akwatin zabe a wata mazaba.

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cafke matasan da suka aikata hakan.

Zaben jihar Ekiti na da muhimmanci kasancewar ita ce kadai jihar da ke karkashin mulkin jam’iyyar adawa ta PDP daga cikin jihohin Yarabawa. Wanda hakan ya sa ita jam’iyya mai mulki APC ke kokarin ganin ta samu nasarar kwace wannan jiha.

Domin karin bayani saurari hira da Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Kidayar Kuri’u a Zaben Jihar Ekiti - 3'48"