An Fara Kidayar Kuri'u Bayan Kammala Babban Zaben Ghana

Babban zaben Ghana

Ranar Litinin 7 ga watan Disamba ne aka gudanar da zaben shugaban kasar Ghana da na ‘yan majalisar dokokin kasar mai kujeru 175.

Nan take bayan kammala kada kuri’a a babban zaben kasar ta Ghana da ke yammacin Afrika aka fara kidayar kuri’u, kuma ana sa ran nan bada jimawa ba za a fara samun sakamakon zaben.

Gabanin soma zaben wakilin Muryar Amurka Ridwan Abbas ya zagaya wasu cibiyoyin zabe inda masu kada kuri’a suka kafa dogayen layuka, wasu ma a nan suka kwana don su sami damar yin zabe saboda a cewarsu zaben na da muhimmanci.

Jami’an zabe a wasu cibiyoyi sun ce komai ya tafi daidai kamar yadda aka tsara, ko da ya ke an samu rahoton harbe-harbe a gundumar Awutu Senya da ke jihar tsakiya ta Ghana har wasu su ka jikkata.

Saurari cikakken rahoton Ridwan Abbas.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Kidayar Kuri'u Bayan Kammala Babban Zaben Ghana