.'Yan Tawayen M23 Sun Fara Shawarwarin Sulhu Da Gwamnatin Kwango

'Yan tawayen kungiyar M23 suke jigilar kaya

An fara shawarwarin sulhu tsakanin ‘yan tawayen kungiyar M23 da kuma jami’an gwamnatin kasar Kwango Kinshasa.

An fara shawarwarin jiya lahadi a Kampala babban birnin Uganda cikin wani yanayi na tankiya, a bayanda wakilin kungiyar ‘yan tawaye ta M23, Francosi Ruchongoza, yayi zargin cewa fitinar ta taso ne saboda rashin shugabancin kwarai.

Amma ministan harkokin wajen Kwango Raymond Tshibanda, wanda ya wakilici gwamnati, ya bayyana rashin jin dadin kalaman.

A makon jiya ne kungiyar ‘yan tawayen ta M23 ta janye daga birnin Goma, amma tayi gargadin cewa zata sake kama shi muddin gwamnati bata fara shawarwarin sulhu da ita kamar yadda tayi alkawari tunda farko ba.

A halinda ake ciki kuma, dakarun gwamnatin Somalia da sojojin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka sun kwace garin Jowhar daga hanun mayakan sakai na al-shabab.
Shaidun gani da ido suka ce a jiya lahadi da safe ne dakarun suka shiga garin suka gwabza dan karamin fada da mayakan sakan, daga bisani suka kama garin baki daya.