An Fara Yi Wa Jami’an Tsaron Najeriya Binciken Kwakwalwa

Sojojin Najeriya

Rundunar tsaron farin kaya ta Najeriya ta fara binciken kwakwalwa tsakanin jami’anta da nufin tabbatar da lafiyarsu da kuma inganta aikin.

Ganin yadda ake yawan samun sakin bindiga a kuskure da kashe rayukan farin kaya da basu ci ba basu sha ba, yasa kungiyoyin kare hakkin BIl’adama suka rika kira da a binciki lafiyar kwakwalwar wasu jami'an tsaro da suke zargin cewa, suna wuce gona da iri da kuma harbi ba bisa ka'ida ba.

Rundunar farin kaya ta dauki matakin tabbatar da lafiyar jami’an ne ta wajen gudanar da jarrabawa da ta shafi tunani da kwakwalwa.

Mai Magana da yawun rundunar Ali Abari Fika wanda yake daya daga cikin jami'an sashin binciken kwakwaf na rundunan da aka turo jihar Adamawa ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne ganin abinda ya faru a wadansu jihohin kasar da ya hada da yadda wani jami’in tsaro a Lagos ya yi barazanar cewa zai je ya kashe wani ya kuma je ya aikata kisan.

Ana ganin daukar wannan matakin zai taimaka wajen kare martabar aikin soja da kuma kara samun kwarewa a aikin da zai zama da muhimmaci wajen cimma guri.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz daga Yola,

Your browser doesn’t support HTML5

Binciken Kwakwalwar Jami'an tsaro-3:20"