An Fara Zaman Makoki A Jamhuriyar Benin

Hagu zuwa Dama: Sakataren Hukumar raya Tabkin chadi, Sanusi I. Abdullahi; Shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin; shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya; shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar; shugaba Idris Deby na Chadi; wakilin shugaban Kamaru, minist

Kasar Jamhuriyar Benin ta soma zaman makoki na mako daya don juyayin rasuwar tsoho shugaban kasar Mathew Kerekou da ya rasu jiya Laraba.

Ba’a dai bada wani cikakken bayanin abinda ya janyo ajalin nashi ba, amma tarihinsa ya nuna cewa ya samu horaswar aikin soja ne a birnin Paris na Faransa wanda bayansa ne ya koma kasar tasu wacce a wancan lokacin ake kiranta da suna “Dahomey.”

A cikin shekarar 1972 ne Kerekou ya kwace ragamar mulkin kasar ta hanyar juyin mulki inda ya aiwatarda ita a matsayin kasar dake bin akidar Kwaminisanci, sannan ya chanja mata suna zuwa “Benin.”

Bayanda akidar kwaminisancin taki ci ne, Kerekou yayi watsi da ita, kuma ya maida kasar a bisa akidar demokradiya inda Benin ta zama daya daga cikin kasashen Afrika na farko da suka gudanarda zaben shugaban kasa na siyasa tsagaronta.

An kada shi a zaben da aka yi na 1991 amma ya sake samun nasara a 1996 inda kuma yaci gaba da zama kan karagar mulki har lokacinda sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar ya tilasta mishi sauka daga mulki a shekarar 2006.