An Fito Da Sabbin Tuhume-tuhume Akan Kisan George Floyd

An gabatar da wasu manyan sabbin tuhumce-tuhumce jiya Laraba, a batun kisan George Floyd, wani bakar fata wanda ya mutu a makon da ya gabata a hannun ‘yansanda a birnin Minneapolis da ke jihar Minnesota.

Atoni Janar na jihar ta Minnesota Keith Ellison, ya tuhumi Derek Chauvin da laifin kisa na mataki na 2, wato tsohon dan sandan nan farar wata wanda ya danne wuyar Mr Floyd da gwiwarsa duk da cewar yana ta ihun cewa baya iya numfashi.

Ellison ya kuma tuhumi sauran tsoffin ‘yansandan su uku, wadanda ke wurin da lamarin ya faru, kuma basu hana wannan kisa na mataki na 2 din ba. Wato da Tou Thao, Alexander Kueng da Thomas Lane. An dai kori dukkanin tsoffin ‘yansanda daga wurin aiki bayan da Floyd ya mutu, amma Chauvin ne kawai ake tuhuma da aikata babban laifi.