An Ga Watan Ramadan A Saudiyya

Hukumomi sun umurci a fara azumi daga gobe Asabar, 1 ga watan Maris.

A yau Juma'a rahotanni na cewa an ga jinjirin watan azumin Ramadan a Saudiyya.

Hukumomi sun umurci a fara azumi daga gobe Asabar, 1 ga watan Maris.

Shafin Haramain Sharifain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce, "an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1446 wato shekarar 2025 a Saudiyya."