An Gano Wasu Yara Da Aka Sace A Nijer

Yaran Nijer da aka gano

A cikin daren jiya ne a ka gano yaran nan da a kayi garkuwa da su a Birnin N'Konni tun ranar Asabar din da gabata, bayan da masu garkuwar suka ce sai an basu kudi sannan su sako yaran.

An gano wasu yara biyu da wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba, suka yi garkuwa da su a birnin N'Konni da karfe 9 da minti 18 na daren jiya litinin.

A lokacin da mahukunta suka je yiwa iyayen yaran da jama'ar gari da suka yi tururuwa a wata unguwa barka da gano wadanan yaran, Magajin garin Birnin N'Konni, Docteur Assumane Sumaila, ya bayyana cewa barayin sun bugawa iyayen yaran waya akan su kai masu kudin fansa a Najeriya, amma rashin dabararsu ta sanya aka kai ga ceto yaran.

Naira Miliyan 10, kwatankwacin Sefa miliyon 16 ne barayin suka bukaci a kai masu kafin su sako yaran.

Shugaban gundumar birnin N'Konni, shugaban dukkan jami'an tsaro na wannan gundumar kuma, malam Ibrahim Abba Lele ya tabbatar da cewa ba a ba barayin ko sisi ba. Allah ne ya taimaka aka gano su. Ba a dai kai ga kama barayin ba, amma ana kan gudanar da bincike, a cewar malam Ibrahim Abba.

Daya daga cikin wadanda a kayi garkuwa da dansa, ya bayyana farin cikinsa bayan ganin an sako yaran ya kuma yaba da kokarin da jami’an tsaro da sauran jama’a suka yi wajen ganin an gano yaran.

Wannan lamarin ya sa hukumomi na bariki da na gargajiya na Birnin N'Konni, yin kira ga al'ummar wannan gundumar, da ta sa ido sosai akan abubuwan dake faruwa, ganin cewa an soma ganin wadansu dabi’u a wannan yankin, da ba'a saba gani ba, da suka shafi sha'anin tsaro.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gano Wasu Yara Da Aka Sace A Nijer - 3'58"