An Garkame Tsohon Magajin Garin Maradin Jamhuriyyar Nijar

Shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou

Sakamakon kama Kassum Mukhtar shugaban jam’iyya adawa ta CPR na yanzu kuma tsohon Magajin Garin Maradi, magoya bayansa sun ce dalilan siyasa ne kawai.

Wakilin Muryar Amurka ya hada mana rahoton cewa magoya bayansa sun tabbatar da cewa an kama shi ne kawai saboda dalilan siyasa. Sun kuma sun tabbatar da cewa shekaru hamsin da suka gabata a tarihin garin Maradi Nijar ba a sami wani Magajin Garin da yayi aiki kamarsa ba.

Alhaji Ibrahim Muhamman Maiturare ne ya bayyana haka a matsayinsa na Mai kula da sashin kwamitin tsare-tsaren Jam’iyyar CPR din wacce shi Kassum din ke cikinta.

Ya tabbatar da haka tare da cewa zaben 2016 suna nan zasu tabbatar ko Kassum yana daure ko yana sake zasu yi zabe cikin nasara tare da bada mamaki. Sannan ya kara da cewa, “Shekaru uku kacal da Mukhtar din yayi yana mulkin Maradi, ko jariri zai iya nuna ayyukan da yayi a lokacin da yake Magajin Garin.

Rahotanni na nuna cewa an kama shi Kassum din da zargin ya ci kudi amma kuma ba a sami makamar dafawa ba don cimma hujjar hakan.

Your browser doesn’t support HTML5

Maradin Nijar