An Gindaya Sabbin Matakan COVID-19 a Hong Kong

Wasu mutane sanye da takunkumin fuska a Hong Kong

Daga cikin sabbin matakan kariya da aka gindaya a Hong Kong sun hada da tilasta amfani da takunkumin rufe baki da hanci ga masu amfani da motocin haya.

Za kuma a ci tarar wanda ya karya dokar har dalar Amurka 645, dala dubu 5,000 kenan kudin Hong Kong.

An haramtawa gidajen cin abinci karbar abokan hulda a ciki bayan 6 na yamma, haka su ma wuraren motsa jiki da gidajen rawa da kallo zasu kasance a rufe domin bin umurnin shugaba Carrie Lam wadda ta kuma sake takaita taruka daga mutum 50 zuwa 4 kawai.

Shugabar Hong Kong, Carrie Lam

Sabbin sharudan sun kuma tilasta rufe shararren filin wasan yara na Disneyland a Hong Kong wanda aka sake budewa a watan jiya.

Cibiyar kasuwancin ta Asiya ta sanar da sababbin kamuwa da COVID-19 52 a jiya litinin, 41 daga cikinsu daga cikin gida suka kamu wanda haka ya sa hukumomi suka bada sanarwa yiwuwar kara yaduwar cutar sosai.

Akalla mutum 1500 ne suka kamu da coronavirus a birnin tun barkewar annobar.