An Hallaka Mutane A Hare-Haren Bam Da Daren Jiya A Jos

  • Ibrahim Garba

Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya Solomom Arase

Bayan wani dan lokaci na kwanciyar hankali a Jos, babban birnin jahar Filato, jiya da dare an kai wasu hare-haren bam biyu, wadanda su ka hallaka mutane.

Wasu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba, sun hallaka mutane da hare-haren bama-bamai da daren jiya a Jos, babban birnin jahar Filato.

Wakiliyarmu a Jos Zainab Babaji ta shaida ma abokin aikinmu Ladan Ibrahim Ayawa cewa bam na daya ya tashi ne da misalin karfe tare na dare a wani wurin cin abinci da ake ma lakabi da Sha Shagalika, mallakin wata mata mai suna Hajiya Talatu, a Bauchi Road – wato kusa da tashar motar zuwa Bauchi.

Zainab ta ce wadanda ta zanta da su sun ce sun ga gawarwaki a ciki da wajen shagon. Ta ce saboda kowa ta kansa yak e yi bayan harin, wadanda ta zanta da su sun ce bas u iya kirga gawarwakin ba a wurin cin abincin.

Ta ce bam na biyun kuma ya tashi ne ‘yan dakikoki kadan bayan na Bauchi Road din. Kuma ya tashi ne a ‘Yan Taya daura da inda Sheikh Sani Yahaya Jingir ke gabatar da tafsirin watan Ramadan. Zainab ta ce wanda ya mana bayani y ace maharin ya je wurin ne da farin kaya ya harba bam, sai kawai aka ji bam kuma ya tashi. To saidai ta ce wanda ya ma ta bayani y ace bai ga gawa da idanso ba a lokacin kodayake dare ne don haka ta yiwu akwai gawa ko gawarwaki . Ta ce ta yi ta kiran jami’an tsaron don jin abin da su ka sani da kuma matakan da su ke daukawa amma ba su dauki waya ba.

Your browser doesn’t support HTML5

An Hallaka Mutane A Hare-Haren Bam Da Daren Jiya A Jos -3'3''