An Haramta Zanga Zanga, Gangamin Murnar Lashe Zabe a Bauchi

Wasu 'yan Najeriya a lokacin da suke murnar lashe zabe a 2019

Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta hana duk wani nau’in gudanar da zanga zanga da ta shafi batun siyasa.

Wannan sanarwan ta biyo bayan zanga zangar lumana ce wanda kungiyoyi iri daban -daban suka dauki tsawon kwanaki uku suna gudanarwa da nufin tilastawa hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon zaben gwamna wanda Jam’iyar PDP ta samu rinjayen kuri’u.

Amma hukumar zaben INEC ta sanar cewa zaben bai kammala ba, ta kuma saka 23 na wannan wata a matsayin ranar da za a sake zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ake takaddama akai.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Bauchin, DSP Kamal Datti, ya ce gudanar da zanga zangar ka iya rikidewa zuwa wani abu da ba zai yi kyau ba ga zaman lafiyan jihar.

Alhaji Yanuwa Zainabari, Sakataren watsa labarai na jam’iyar PDP a jihar Bauchin ya nuna alhininsa kan yadda INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, yana jaddada cewa su za su samu nasara.

Ita ma jam’iyar APC mai mulki a jihar, sakataren kwamitin yakin neman zaben gwamnan, Alhaji Balarabe Shehu Elelah ya ce a shirya suke domin shiga zaben da za’a saken.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhamamd daga Bauchi:

Your browser doesn’t support HTML5

An Haramta Zanga Zanga, Gangamin Murnar Lashe Zabe a Bauchi - 2'56"