An Jefa Shugaban Yakin Neman Zaben Trump, Paul Manafort A Kurkuku

Paul Manafort a kotun tarraya

An jefa tsohon shugaban kwamitin yakin neman zaben Shugaban Amurka Donald Trump Paul Manafort gidan yari jiya Jumma'a, bayan da wani kwamitin masu taya alkali yanke hukunci na gwamnatin tarayya ya same shi da laifin kokarin karkatar da shaida, lokacin da aka sake shi bisa sharuddan beli.

Manafort, dan shekaru 69 da haihuwa kuma na farko cikin tsoffin mukarraban Trump da aka jefa kurkuku, an same shi da laifi a makon jiya a wasu sabbin tuhumce-tuhumce biyu, na kokarin hana shari'a ta yi aikinta da kuma hadin baki don gurgunta tsarin shari'a, wanda ke da nasaba da yinkurin da ya yi a watannin baya-bayan nan, na karkatar da ra'ayin wasu shaidu biyu da aka saya sunayensu.

Da yake Magana da manema labarai a harabar Fadar White, Trump yace abinda ake yiwa Manafort ba daidai bane.

Trump yace, “Sun koma shekaru goma sha biyu da suka shige, suna neman abinda ya aikata shekaru goma sha biyu da suka shige? Paul Manafot yayi mani aiki na kankanen lokaci ne. Ya yiwa Ronald Reagan, ya yiwa Bob Dole aiki, ya yiwa John MacCain aiki, ya yiwa ‘yan jam’iyar Republican da dama aiki. Ya yi min aiki na tsawon kwanaki arba’in da tara ko makamancin haka, dan kankanen lokaci.Raina ya baci da wadansu mutane domin suna binciken abinda wani ya aikata shekaru goma sha biyu da suka shige. Wannan ba daidai bane.”

Manafort dai, ya fada jiya Jumma'a, cewa bai aikata wani laifi ba dangane da wadannan tuhumce-tuhumcen biyu.

To amma wata alkalin kotun tarayya mai suna Amy Berman Jackson, wadda ta yi nuni da zarge-zargen kokarin karkatar da ra'ayin shaidun, ta bayar da umurnin a tsare shi a gidan yari har sai lokacin da za a yi masa shari'a a watan Satumba, wanda hakan ya zo daidai da bukatar mai shari'a na musamman Robert Mueller, ta soke belin da aka ba shi, Manafort