An Kaddamar Da Fim Din Da Ke Fadakar Da Jama'a Muhimmancin Zaman Lafiya A Nijar

Majigin Caravane de la paix CINE NOMADE

A Nijr, an gudanar da bikin kaddamar da ayarin zaman lafiya inda cibiyar fina-finai ta CINE NOMADE da tallafin ofishin jakadancin Amurka a Nijar za ta zagaya jihohin kasar da nufin tattaunawa da jama’a akan batun zaman lafiya musamman matasa.

Matsayin fina-finai a wajen al’umma da tasirin sakonnin da suka kunsa wajen canza tunanin jama’a ya sa fitacciyar mai tsara fina-finan nan ‘yar Nijar Aicha Macky ta bullo da wannan shiri na ayarin zaman lafiya da aka yi wa lakabin Caravane de la paix CINE NOMADE, wanda a karkashinsa za a wayar da kan matasa a game da batun zaman lafiya.

Wannan fim da a watannin baya ya zagaya wasu kasashen Afirka da na yammacin duniya, labari ne na zahirin rayuwar wasu matasan Damagaram.

Ba ya ga motocin jigila da majalisun matasa, ayarin na caravane CINE NOMADE na da niyyar sauka a makarantun sakandare da jami’o’in wannan kasa domin jin damuwoyi da shawarwarin dalibai.

Shugaban kungiyar daliban jami’ar Yamai Bakin Batoure Almoustapha, ya jaddada goyon baya ga wannan yunkuri.

Bikin kaddamar fim din CARAVANE

Wakilin matasan jihar Maradi a wurin bikin kaddamar da wannan ayari Tassiou Bakoye, ya ce su kam faduwa ta zo dai dai da zama dole ne a rike shi hannu biyu-biyu.

Kasar Amurka ta taka rawa wajen tsara wannan sabuwar tafiya mai hangen karfafa kwanciyar hankali a kasa, kamar yadda Stephen Dreikorn ya bayyana.

“Kasar Nijer ta bude wani sabon babi a tarihinta inda a karon farko wani zababben shugaban kasa ya canji wani shugaban da ya yi mulki ta hanyar dimkokradiyya, duk da wannan ci gaba da aka samu akwai bukatar hada guiwa da matasa domin taimaka wa Nijer ta sami damar murmurewa ta kuma sami wadata, saboda haka muka shiga wannan tafiya don ganin an cimma gurin da aka sa gaba,” a cewar Dreikorn.

Fim din Caravane- Nijer

Watanni akalla 10 za a shafe ana haska wannan Fim na Zinder a cikin motocin jigila da majalissun matasa, da makarantu, da jami’o’i a dukkan fadin kasar, hade da mahawarori akan zamantakewar al’umma da zummar tattara shawarwarin matasa da na shugabannin addinai da sarakunan gargjiya wadanda a karshe za a gabatar da su ga hukumomi don ganin an dinke dukkan wata baraka da ke barazana ga zaman lafiya.

Saurari Rahoton Souley Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Fim Din fadakarwa Kan Batun Zaman Lafiya