Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daraktan “Izzar So” Nura Mustapha Ya Rasu


Marigayi Nura Mustapha
Marigayi Nura Mustapha

Nura ya rasu ne a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, an kuma yi jana’izarsa da misalin karfe 11 na safe.

Allah ya yi wa Daraktan fim mai dogon zango na “Izzar So” Nura Mustapha Waye rasuwa.

Jarumin fim din na “Izzar So” Lawan Ahmad ne ya bayyana rasuwar Nura a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi.

“Innalillahi wa’innailaihirrajiun. Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye, Director IZZAR SO.” Ahmad ya wallafa ya ce.

Nura ya rasu ne a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya an kuma yi jana’izarsa da misalin karfe 11 na safe.

Lawan Ahmad, hagu, Ali Nuhu, tsakiya, marigayi Nura Mustapha, dama (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)
Lawan Ahmad, hagu, Ali Nuhu, tsakiya, marigayi Nura Mustapha, dama (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)

“Allah ya yafe masa kurakuransa Amin, Allah ya sa idan ta mu ta zo mu cika da imani. Amin.” Ahmad ya kara da cewa.

Nura Mustapha, darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana'antar ta Kannywood.

Fim din na Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya.

Kiyasi da aka yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa fim din shi ne ya fi yawan masu kallo a dandalin YouTube da ake nuna fim din.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG