An Kaddamar Da Rundunar GARSI Don Yaki Da 'Yan Ta'adda a Yankin Sahel

Rundunar GARSI

A ci gaba da neman hanyoyin murkushe matsalar ta’addancin da ya addabi yankin Sahel hukumomi a jamhuriyar Nijer sun kafa wata sabuwar runduna ta musamman da ake kira GARSI mai kunshe da jami’an tsaron jandarma zalla wace za ta yi aiki kafa-da-kafada da wasu takwarorinta na nahiyar Turai.

An gudanar da bikin kaddamar da rundunar GARSI ne a farfajiyar makarantar horarda jami’an tsaron jandarma dake unguwar Kwaratagi a Yamai, wace hukumomin tsaron Nijer suka kafa takanas da nufin karfafa matakan yaki da ta’addanci kamar yadda wani taron ministocin tsaro da na cikin gidan kasashen Sahel da ya gudana a shekarar 2016 a garin N’djamena ya shawarci gwamnatocin kasashen G5 SAHEL a kai.

Da yake jawabi a yayinda yake jagorantar bikin kaddamar da ayyukan wannan sabuwar rundunar, Ministan tsaron kasar Nijer Kalla Moutar, ya bayyana cewa ana fuskantar kalubalen tsaro mafi girma a tarihin kasashen saboda haka dole ne su dage don ganin sun yi nasara a yakin da suka sa gaba.

“Wannan ita ce hanya mafi a’ala da za ta bamu damar sakawa sojojinmu da suka kwanta dama a fagen daga kamar yadda muke da nauyin samarda tsaron da zai baiwa talaka damar gudanar da harkokinsa hankali kwance,” inji ministan.

A cewar jagorar tawagar tarayyar Turai a Nijer Dr. Denissa Ionete, Miliyan 5.8 na euro kungiyar tarayyar Turai ta kebe domin wannan rundunar, kudaden da aka yi amfani da wani bangarensu don samarda kayan aiki na fiye da miliyan 3 na euro wadanda suka hada da motoci da babura da dai sauran kayayyakin amfanin mayakan.

Gamsuwa da yanayin huldar dake tsakanin kasar Nijer da kungiyar tarayyar Turai da a daya bangaren yarda da jajircewar jami’an tsaron jandarma wajen yaki da masu aikata miyagun ayyuka ya sa wannan kungiya amincewa daukar dawainiyar wannan rundunar ta GARSI, wace a gwajin da aka yi a yayin bikin yayen dakarunta alamu ke nunin sun lakanci dubarun yaki irin na zamani.

Ga karin bayani a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Rundunar GARSI Don Yaki Da 'Yan Ta'adda a Yankin Sahel - 2'04"