An Kaddamar Da Shirin Kayata Birnin Maradi

A Jamhuriyar Nijar an kaddamar da shirin kayata birnin Maradi a wani mataki na maida birnin zuwa cikakke birni na zamani.

A Jamhuriyar Nijar, an kaddamar da shirin kayata birnin Maradi a wani yunkuri da gwamnati ke yi na bunkasa biranen kasar.

Wannan wani mataki ne na yin tuni da ranar da jamhuriyar ta Nijar ta zama jamhuriya a karakashin shirin da aka yiwa take da “Maradi Kwalliya.”

“Burin shi ne a kayata wadannan birane a wannan jamhuriya ta bakwai.” In ji Fira Minista Briji Rafini a lokacin da ya ke dasa tubalin kaddamar da shirin.

Shugaban Kwamitin Tsara ayyukan kayata garin na Maradi, Minista Malam Kala Hankarau, ya ce ayyukan da za a gudanar sun shafi gina hanyoyi da filin kwallo da na kokuwa da na wasan kwaikwayo.

A cewar Ministan cikin watanni takwas a ke so a kammal ayyukan wadanda za a yi su na zamani.

Mutane da dama a garin na Maradi sun nuna gamsuwar da wadannan ayyukan da za a fara gudanarwa, sun kuma nuna farin cikinsu.

“Muna masu alfahari da wannan shiri, mun duba mun ga abin da aka yi a birnin Doso.” In ji wani mazaunin garin Maradi.

A shekarar 2013 aka kaddamar da irin wannan aiki a Niamey N’yala, sannan a shekarar 2014 aka kaddamar da na Dosso Soga.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Shirin Kayata Birnin Maradi