An Kaddamar Da Wani Shiri A Nijer Don Magance Mace-Macen Mata Da Yara

Hukumomin jamhuriyar Nijer da hadin gwiwar gwamnatin kasar Amurka sun kaddamar da wani sabon shiri da ake kira Amplify PF da zummar fadakar da jama’a muhimmancin mutunta tsarin saka tazara a haihuwa,

A yau hudu ga watan Afrilu, dimbin jama’a suka hallara domin kaddamar da wani shiri na musamman da ake kira Project Amplify PF da turanci a farfajiyar asibitin haihuwa na unguwar ‘Yantala dake birnin Yamai. A karkashin shirin ne gwamnatocin Nijer da Amurka ke hangen magance matsalar mace macen mata da yara, lamarin da likitoci ke dangantawa da rashin saka tazara tsakanin haihuwa.

Miliyan 10,000 na CFA ne kasar Amurka ta hanyar hukumar USAID za ta kashe domin wannan shiri na tsawon shekaru 5 wanda kuma za a aiwatar a yankunan Yamai, da Zinder da nufin sassauta wahalhalun jama’a a bisa la’akari da yadda matakin ka iya baiwa yara damar samun ilimi yayinda iyayensu mata zasu samu damar gudanar da wasu ayyukan ci gaba kamar yadda jakadan Amurka a Nijer Eric P. Whitaker ya bayyana.

Ministar ci gaban mata da kare yara kanana. Elback Zeinabou Tari Bako, ta jinjinawa wannan yunkuri da take ganin yana da alfano sosai ga rayuwar iyali.

Uwargidan shugaban kasar Nijer Dr. Malika Issouhou, dake matsayin uwa a wannan buki ta yi kira ga shuwagabanin al’umma wato sarakunan gargajiya, da malamai, da kafafen yada labarai, da kungiyoyi masu zaman kan su, akan su dage wajen fahimtar da jama’a illolin dake tattare da haihuwar rurutsa.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Wani Shiri A Nijer Don Magance Mace-macen Mata Da Yara - 2"57"