An Kafa Dokar Hana Zirga-zirga a Karamar Hukumar Bassa Da Rikici Ya Addaba

  • Ibrahim Garba

Buhari a Fadar Gwamnan jahar Filato

'Yan kwanaki kadan kawai bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyukan cigaba da kuma jaddada zaman lafiya a jahar Filato, sai gashi kuma an yi jina-jina a Karamar Hukumar Bassa.

A yinkurinta na kawo karshen mummunan rikicin nan da ya auku a Karamar Hukumar Bassa ta jahar Filato, gwamnatin jahar ta kafa dokar takaita zirga-zirga daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a Karamar hukumar Bassa, inda rahotannin ke nuna cewa bayan jina-jinar da aka yi tsakanin al’ummomi, an kuma tsinci gawarwakin ‘yan bindiga a wata fafatawar da su ka yi da jami’an tsaro, wadanda su kuma su ka rasa mutane akalla biyu.

Sanarwar kafa dokar takaita zirga-zirgar, wadda Sakataren Gwamnatin Jahar Filato Rufus Bature ya sanya wa hannu, ta kuma tabbatar da cewa baya ga rasa rayuka da raunana jama’a da dama, rikicin ya kuma yi sanadin kona kaddarori da wuraren ibada da muhallai a garuruwan Dungu da Rafiki da sauransu da ke yankin.

Kwamishinan Yada Labaran Gwamnatin jahar Filato Mr. Yakubu Datti ya ce tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da wannan matakin da aka dauka. Ya ce an fara damke wasu da ake zargi da hannu a wannan kazamar rigimar. Ya ce gwamnatocin jahohin Filato da Kaduna na aiki tare don shawo kan wannan matsalar. Sai dai ya noke da aka tambaye shi adadin mutanen da aka kashe.

Ga Zainab Babaji da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Dokar Hana Zirga-zirga a Karamar Hukumar Bassa Da Rikici Ya Addaba