An Kafa Dokar Ta Baci A Garin Wukari Da Kewaye Da Ke Jihar Taraba

Bayan da aka kai hari akan tawagar dan takarar gwamna jam'iyyar APC a jihar Taraba, an kafa dokar hana fita daga yamma zuwa safiya. Jami'an 'yan sanda sun kaddamar da bincike kan wannan harin.

Yanzu haka an Kafa dokar hana fita, wacce za ta soma aiki daga karfe shida na maraice zuwa shida na safe a garin Wukari da kewaye.

Hakan ya biyo bayan farma tawagar ‘yan jam’iyyar APC da wasu gungun ‘yan bangan siyasa suka yi a Wukari, inda dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC Sani Abubakar Danladi da jakadan Najeriya a kasar Trinidad da Tobago Ambassada Hassan Jika Ardo da wasu kusoshin jam’iyar suka tsallake rijiya da baya, yayin da aka raunata wasu da dama da kuma kona motoci.

A wajen wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba Jalingo, ‘yan tawagar da suka tsallake rijiya da bayan sun bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta bincike kan wannan harin.

Sai dai mai ba wa gwamnan Jihar Taraba shawara a kan harkokin siyasa Abubakar Bawa, ya musan ta zargin cewa da hannun gwamnatin jihar a harin da aka kaiwa tawagar ta APC.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-Aziz:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Dokar Hana Fita A Garin Wukari Da Kewaye, JIhar Taraba