An Kafa Kungiyar Hana Shan Miyagun Kwayoyi A Najeriya

Shan miyagun kwayoyi da jabun magunguna su na cikin matsalolin da ke damun gwamnati, abin da yanzu haka wata kungiya mai zaman kanta ta dauki alkawarin taimaka gwamnati domin magance wannan matsalar.

An kaddamar da wata kungiya ta sa kai da za ta taimaka wajen hana sha da kuma wayar da kan jama’a game da muggan kwayoyi a Najeriya.

Tsohon shugaban kungiyar likitocin hada magunguna ta Najeriya, Dr. Ahmad Ibrahim Yakasai, wanda shi ne shugaban kungiya, ya ce makasudin kafa wannan kungiyar shi ne, wayar da kan jama’a musanman matasa akan illar shan miyagun kwayoyi.

Har ilau yau kungiyar za ta dukufa wajen tabbatar da ganin an kawo karshen sayar da jabun magunguna a kasar.

Kungiyar mai suna Safe Medicine Foundation zata taimaka wa gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi wajen tabbatar da aiki da dokokin inganta shan magunguna a kasa.

Saurari cikakken rahotn Babangida Jibril:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Kungiyar Hana Shan Miyagun Kwayoyi A Najeriya