Karin Bayani Kan Hari a Ofishin Hukumar EFCC Na Zone 7 Abuja

EFCC

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a sashen ofishin EFCC dake kula da kayan da hukumar ta kwato daga masu yin zarmiya da aikata magudi da kudaden kasashen waje da binciken manyan 'yan siyasa da manyan hafsan sojoji da suka yi ritaya

Harin da aka kai daya daga cikin ofisoshin EFCC na anguwar Zone 7 Abuja bai sauya yanayin hada hada ba hatta a babban ofishin hukumar dake Adetokunbo Ademola a Wuse 2 ba.

Ofishin na Zone 7 na kula da lamuran da suka shafi fitar da kudin haram ne. Inji kakakin hukumar ta EFCC sun kaiwa 'yansanda rahoton abun da ya faru domin su cigaba da binciken lamarin.

Bayan gumurzun da jami'an EFCC dake tsaron ofishin suka yi da 'yanbindigan, maharan sun bar wata wasika baya inda suke barazanar hallaka Ishaku Daru jami'in dake binciken manyan badakaloli da suka hada da tsoffin jami'an sojoji da manyan 'yan siyasa

Dangane da cewa ko harin yana tabbatar da ikirarin da shugaban hukumar ya yi ne na cewa cin hanci da rashawa na yaki da hukumar, kakakin Uwujeren yace a'a shi ba zai dora wani bayani ba sai an kammala bincike..

Tsohon shugaban hukumar Nuhu Ribadu yace sun sha fuskantar barazana a aikin. Yana mai cewa aikin ba karami ba ne. Inji shi "zaka yi fada da mutane. Za'a kika. Za'a yi yaki da kai. Za'a hanaka komi. Amma aikin kusan ibada ce. Ka yi aikin Allah ne. Ka taimakawa talakawa...Na yi wannan aikin. A ciki babu abun da bamu gani ba. Za'a yi kokari a baka kudi. A nemi kasheka. Za'a ma koreka daga aikin. A hanaka zama a kasarka..."

Nuhu Ribadu ya kira jama'a da su ba gwamnatin Buhari goyon baya musamman a yaki da cin hanci da rashawa..

A 'yan kwanakin baya ma an harbi jami'in hukumar a Fatakwal Austin Okoh amma ya tsallake rijiya da baya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Hari Kan Wani Bangaren Ofishin Hukumar EFCC Na Zone 7 Abuja - 2' 30"