An kai sabon hari a kauyen Rukubi jihar Nasarawa har an kashe mutane goma sha shida

Gawar mutane da aka kashe lokacin rikici

Kimanin wajen mutane goma sha shida a kashe a kauyen Rukubi cikin karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa. Jiya da safe yayin da mutane suka tashi wasu na shirin zuwa aiki wasu kuma na kokarin zuwa gonakansu sai kwaram wasu da bindigoji suka farma kauyen suna harbi. Sun kashe mutane goma sha shida nan take sun kuma kone gidaje wajen ashirin.

Wani ganao ya ce ya kirga gawarwaki goma sha shida a cikin kauyen ban da na bayan gari. Wasu da aka zanta da su sun ce basu san komai ba sai suka fara jin harbe-harbe da safe. Ta dalilin haka ya sa sauran jama'a suka fantsama cikin daji domin su ceci rayukansu.

Kawo lokacin rahoton nan jami'an tsaro basu da masaniya kan lamarin kamar yadda Zainab Babaji ta bayyana a rahotonta.

Your browser doesn’t support HTML5

An kai sabon hari a kauyen Rukubi jihar Nasarawa