An Kai Sabon Hari Kan Cibiyar Masu Kula Da Cutar Ebola A Congo

Wasu wadanda ba'a san ko su waye ba, sun kai hari kan cibyar masu kula da cutar Ebola da ke kasar Congo, inda suka hallaka dan sanda daya.

Wasu mahara dauke da makamai sun far ma wata cibiyar kula da masu dauke da cutar Ebola a kasar Congo, kasa da mako guda, bayan da aka sake bude cibiyar, sanadiyar wani hari na daban da aka kai a baya.

Harin, wanda aka kai da sanyin safiyar jiya Asabar, a garin da ake kira Butembo, ya yi sanadin mutuwar dan sanda daya, sannan wasu ma’aikatan cibiyar da dama sun jikkata.

Magajin garin na Butembo, Sylvain Kanyamanda, ya fadawa manema labarai cewa, jami’an tsaro sun kare cibiyar, har ma sun jikkata daya daga cikin maharan.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ziyarci cibiyar, sa’o’i bayan harin, ya kuma karawa ma’aikatan wurin kwarin gwiwa, kan aikin da suke yi na yaki da cutar ta Ebola mai saurin kisa.