An Kama Dan Morocco Bisa Zargin Kai Hari

Morocco Floods

‘Yan sandan Italiya, sun ce sun cafke wani mutum dan kasar Morocco, wanda ake zargi da hanu a harin da aka kai a ranar 18 ga watan Maris, akan wani gidan tarihin kasar Tunisia, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22.

A yau laraba,’yan sandan sun gayawa manema labarai cewa an kama mutumin ne mai shekaru 22 a garin Gaggiano da ke kusa da birnin Milan. Kuma ‘yan sanda masu yaki da ayyukan ta’addanci ne suka kama shi, yayin da nan gaba kadan ake sa ran ‘yan sanda za su fitar da karin bayani game da mutumin.

Kungiyar IS mai da’awar kafa daular musulunci dai ta dauki alhakin harin, wanda wasu ‘yan bindiga suka bude wuta akan wata mota kirar bas da cike makil da ‘yan yawon bude ido a wajen gidan tarihin da kuma cikin ginin.Harin dai ya halaka wani dan sandan Tunisia guda sannan wasu ‘yan kasashen waje su 21 suka mutu.

‘Yan sanda dai sun harbe biyu daga cikin maharan nan take, kuma an cafke wasu da dama da ke da hanu a harin. Wannan hari ya sa dubban mutane gudanar da zanga zanga a Tunis, babban kasar, domin nuna adawa da tashe-tashen hankula dake faruwa a kasar.