An Kama Magoya Bayan madugun Adawa A Turkiya

PM Turkiyya Reccep Erdogan.

A Yau Talata, kafafan yada labaran kasar Turkiyya sun ce hukumomi sun cafke wasu mutane 35, a wani samame da ya maida hankali kan wasu masu goyon bayan wani Malami da ake zargi da yunkurin hambarar da gwamanbtin Shugaba Recep Tayyip Erodgan.

Samamen wanda aka kai shi a yankin Yammacin birnin Izmir, na zuwa ne kwanaki biyu bayan da masu kada kuri’a suka baiwa mafi yawan ‘yan jam’iyyar AKP ta Erdogan kuri’unsu a zaben ‘yan majalisar da aka yi.

Kamfanin dillancin labaran kasar na Dogan ya ce ‘yan sanda sun kai samamen ne a wurare da dama domin cafke wadanda ake zargi, ciki har da wasu jami’an ‘yan sanda da ke goyon bayan Malamin Islaman nan da ke zaune a Amurka mai suna Fathullah Gulen.

A jiya Litinin, shugaba Erdogan ya yi kira ga kasashen duniya da su mutunta nasarar da jam’iyyarsa ta samu, inda ya soki kafofin yada labaran yammacin duniya da ke yawan sukan tsare-tsaren gwamnatinsa