Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar AKP Mai Mulkin Turkiya ta Samu Rinjaye a Zaben Majalisar Dokoki


Firayim Ministan Turkiya Davutoglu yana gaida magoya baya
Firayim Ministan Turkiya Davutoglu yana gaida magoya baya

Jam'iyyar AKP dake mulkin Turkiya ta sake samun rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar

Jam'iyyar AKP ta shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdowan, ta sami rinjaye da ya bada mamaki a zaben wakilan majalisar dokokin kasar da aka yi gabannin lokacin zabe jiya Lahadi,nasarar da ta maida kasar karkashin mulkin jam'iyya daya, wata biyar bayan data rasa rinjayen da take rike da shi a fiye da shekaru 10.

Bayan da aka kusan gama kidaya dukkan kuri'u a safiyar yau Litinin, alkaluma sun nuna jam'iyyar AKP na da kashi 50 na kuri'un, wanda ake hasashen zai bata akalla kujerru 316 a majalisar mai wakilai 550-gibi maifi girma fiyeda abunda aka yi hasashe. Sakamakon farko farko ya nuna jam'iyyar 'yan hamayya ta CHP da kadan zata dara kashi 25 cikin dari.

Shugaba Erdowan, ya ayyana zaben cikin watan Yuni bayan da jam'iyyar AKP mai mulkin kasar ta rasa rinjayen da take dashi a majalisa, kuma Firayim Minista Ahmet Davutoglu ya kasa kafa gwanatin hadin gambiza.

Sa'o'i bayan da aka rufe rumfunan zabe a jiyan, Erdogan ya kira sakamakon a zaman jama'a sun zabi zaman lafiya da amana. Hakan nan ya kira zaben a zaman sako ga 'yan tawayen kurdawa dake kudu maso gabashin kasar cewa "Babu yadda za'a yi tarzoma ta tafi da tafarkin demokuradiyya."

A gefe daya kuma, Frayim Ministan kasar Davutoglu, ya kira jiyan a zaman "rana ce ta nasara". Ha kazalika yace ta nuna tawali'u.

XS
SM
MD
LG